Header Ads

Wednesday, July 8, 2020

Bulldozer Funtua: : Wane ne zai maye gurbin shugaban EFCC da aka dakatar?

Bayan da gwamnatin Najeriya ta dakatar da Ibrahim Magu daga mukamin mukaddashin shugaban hukumar EFCC ranar Talata, wasu rahotanni a kasar na cewa tuni ya kwashe kayansa daga gidan gwamnatin da yake zaune a ciki a Abuja.
Duk da cewa wata majiya mai tushe ta tabbatar wa BBC cewa har yanzu Shugaba Muhammadu Buhari bai yanke shawara ba kan wanda zai maye gurbin dakataccen shugaban na EFCC, amma rahotanni daga jaridun kasar sun bayyana sunayen mutane da dama da ake gani a cikinsu za a samu wanda zai maye gurbinsa.
Kwamitin da Shugaba Buhari ya kafa ya tuhume shi da aikata laifukan cin hanci da rashawa da rashin biyayya da kuma nuna tsageranci ga ministan shari'ar kasar, dalilan da hukumar da yake shugabanta ta rika amfani da su tana aika mutane da yawa zuwa kurkuku saboda sun aikata laifuka makamancinsu.
A halin da ake ciki, mutane sun fara tofa albarkacin bakinsu kan wasu mutane da suke ganin gwamnati za ta iya nadawa su maye gurbin mukaddashin shugaban na EFCC.
Hasalima ranar Laraba, shafin Twiter na Najeriya ya kaure da ambaton sunan Bala Ciroma, wato Kwamishinan 'yan sandan birnin Abuja a cikin wadanda ake sa ran za su iya samun shugabancin na EFCC.
BalaHakkin mallakar hotoTWITTER
Sauran jami'an tsaron da ake cewa su ma za su iya maye gurbin Mr Magu su ne:

Abba Kyari

Abba KyariHakkin mallakar hotoABBA KYARI/FACEBOOK
Wannan shi ne mutumin da 'Æ´an Najeriya suka lakabawa sunan jarumin yaki da laifuffuka saboda kwarewar da yake da ita ta aikin dan sanda.
Abba Kyari mataimakin kwamishinan Æ´an sandan Najeriya ne a halin yanzu, kuma shi ne ke jagorantar wata runduna ta musamman da babban sufeton Æ´an sandan kasar ya kafa da ke yaki da masu satar mutane domin karbar kudin fansa, da sauran manyan laifukan da suka addabi Æ´an kasar.
An haife shi a ranar 17 ga watan Maris 1975, kuma mazauna Legas za su tuna da shi tun da ya taba rike mukamin shugaban rundunar nan ta musamman mai yakar masu aikata laifuka wato SARS.
Abba Kyari ya shiga aikin É—an sanda ne bayan da ya kammala makarantar horon Æ´an sanda ta Wudil a Kano a shekarar 2000 inda aka tura shi jihar Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya domin fara aiki.

Muhammad Wakili

Muhammad Wakili
Muhammadu Wakili shi ne tsohon kwamishinan ƴan sanda a jihar Kano, amma a bara ya yi ritaya daga aikin. Ya yi farin jini yayin da yake aiki a Kano har ta kai ga mutane sun laƙaba masa sunan 'Singham' - wanda sunan wani jarumin dan sanda mai yaki da masu aikata laifuka ne da ya taka rawa a wani fim na Indiya.
An haifi Mohammed Wakili a ranar 26 ga watan Mayun 1959 a garin Gombe, kuma ya fara aikin ɗan sanda ne bayan ya kammala yi wa ƙasa hidima bayan da ya gama karatu a Jami'ar Maiduguri a 1986.
Bayan horon da ya samu a lokuta daban-daban, an nada Wakili ga matsayin mataimakin Sufeton ÆŠan Sanda (ASP) a 1989 kuma an tura shi rundunonin Æ´an sandan kasar masu yawa inda ya yi aiki.
A cikin wadannan mutum ukun, shi ne kawai ya taba aiki a hukumar ta EFCC saboda ya taba yin aiki tare da tsohuwar shugabar hukumar Farida Waziri.
A halin da ake ciki, Wakili shi ne mai ba gwamnan jihar Gombe shawara kan batutuwan tsaro.

Habu Sani

Habu SaniHakkin mallakar hotoKANO POLICE COMMAND
Habu Sani shi ne kwamishinan Æ´an sanda a jihar Kano mai ci, wanda yawancin mutane suka fi saninsa da sunan 'Kalamu Wahid'.
Gabanin a tura shi Kano, Kwamishinan Æ´an sanda Habu yayi aiki a jihar Bauchi kuma mutane na kallonsa a matsayin wanda bai cika son wargi ba.
Shi ne ya jagoranci jami'an da suka raba Muhammadu Sanusi II daga mukamin Sarkin Kano. kuma shi ne ya fitar da shi daga fada kana ya tabatar da zaman lafiya da tsaro a birnin.
Saboda haka wasu ke yaba ma sa saboda kwarewarsa kan aikin tabbatar da tsaro.
An haife shi a shekarar 1964, kuma shi dan gidan sarautar sarkin Musulmi ne da ke Sokoto a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Ya fara aikin É—an sanda ne a 1992 bayan da aka yaye shi daga Jami'ar Usmanu Danfodio inda ya nazarci ilimin Geography.
Kamar Abba Kyari, shi ma Habu Sani na da kwarewa kan ayyukan tsaro kuma ya taba rike mukamai a sashen bincike da ayyukan sirri na rundunar Æ´an sandan Najeriya.
Ya kuma taba yin aiki tare da Majalisar ÆŠinkin Duniya a matsayin jami'i mai horar da rundunar kiyaye zaman lafiya da aka tura Sudan ta Kudu a shekarun 2006 zuwa 2007.

No comments:

Post a Comment

Popular Feed

Recent Story

Featured News

Back To Top